21 Oktoba 2020 - 16:24
Zanga-Zangar Endsars: An Fara Daukar Matakan Daƙile Munin Da Zanga-Zangar Ke Daɗa Yi

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar gwamnatin jihar Lagos ta biyon sahun ta jihar Edo wajen sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 biyo bayan ci gaba ƙazamtar tarzomar da ake yi a wasu sassa na jihar bayan da zanga zangar neman rusa rundunar nan ta SARS ta rikiɗe ta koma tarzoma da ƙone-ƙone.

ABNA24 : A wata sanarwa da ya fitar, Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya ce dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 4 na yammacin yau Talata inda ya ce dokar ta hana kowa fitowa kan tituna face masu ayyukan hidima da ya zama wajibi su kasance a bisa tituna.

Gwamnan ya ce, ya shiga damuwa yadda ya ga zanga-zangar lumana ta #EndSARS ta rikiɗe ta zama wani abin ban tsoro da ke barazana ga zaman lafiyar al'umma saboda yadda bata-gari suka fake da sunan zanga-zangar suna kashe mutane don haka ya ce ba za su taba bari jihar ta Lagos ta zama tamkar fagen yaki ba.

Rahotanni daga sassan daban-daban na Lagos ɗin na nuni da cewa a al’amura na daɗa taɓarɓarewa sakamakon yadda wasu ɓata garin ke kaiwa jama’a hari da kwace musu kayayyaki, bugu da kari kan sanya wuta a kan dukiyoyin al’umma.

Gwamnatin jihar Edo ce fara ta sanya dokar hana fita bayan wasu 'yan daba da ɓata gari da suka fake da zanga-zangar #endsars ɗin suka kai hari wasu gidajen yari biyu da kuma sake fursunonin da suke ciki bayan kona wasu ofisoshin ‘yan sanda da suka yi.

A babban birnin Tarayyar Nijeriya ɗin ma dai Abuja, an samu irin wannan tarzomar inda ɓata garin suka ci gaba da cin zarafin mutane da kuma ƙone-ƙone lamarin da ya sanya aka fara kiran gwamnatin da ta ɗau matakan da suka dace wajen kare lafiya da dukiyar al’umma.

342/